19 Yuli 2025 - 23:21
Source: ABNA24
Hizbullah: Labanon Na Fuskantar Hatsarin Gaske Guda Uku

Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa, Amurka na son kafa sabuwar yarjejeniya da za ta wanke Isra'ila daga keta haddin da ta yi cikin watanni 8 da suka gabata, wanda matakin farko zai zama kwance damarar makamai (aje makaman Hizbullah). Ya bayyana hatsari uku da ke fuskantar Lebanon.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Baiti (A.S.) - ABNA - ya habarta cewa: Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa, Amurka da mamaya na Isra'ila sun gano cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta na cikin maslaha ne ga kasar Labanon da kuma gwagwarmaya, don haka suka shiga matsin lamba a kokarinsu na yin kwaskwarima. Duk da haka, duk wannan matsin lamba "bai canza yarjejeniyar ba".

A cikin jawabin da ya gabatar a wurin taron tunawa da babban jagoran jihadi, shahidi Ali Karaki "Abu al-Fadl", Sheikh Qassem ya bayyana cewa Washington "na son kafa sabuwar yarjejeniya da za ta wanke Isra'ila daga keta haddin da ta yi cikin watanni 8 da suka gabata, kamar ba su taba faruwa ba".

Sheik Qassem ya kara da cewa matakin farko na wannan sabuwar yarjejeniya ta Amurka shi ne kwance damarar 'yan gwagwarmayar Musulunci a kasar Labanon, inda ya ce dalilin rashin aiwatar da yarjejeniyar da aka rattabawa hannu da kuma yin magana kan wata sabuwar yarjejeniya ita ce kwance damara don tabbatar da Isra'ila.

Sakatare-Janar na Hezbollah ya jaddada cewa Washington tayi karya a lokacin da ta ce "ba ta ba da tabbacin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Lebanon ba," yana mai bayanin cewa gwamnatinta tana "daidaita yakin da Isra'ila da kuma kokarin fadada shi a yankin".

Ya ci gaba da cewa, "A karkashin manufar tsaron Isra'ila, babu wata lungu da ba sa son bincike, mamayewa, da kai farmaki." Ya kara da cewa Gwagwarmaya tana da karfin imani da matsayi, kuma karfin soja yana da alaka da karfin matsayin".

Har ila yau ya bayyana cewa, ana sa ran Gwagwarmaya za ta yi hasara mai yawa idan ta kare kasar Labanon daga mamayar, amma muna da fatan idan muka tashi tsaye, za mu iya rufe kofa a kansu, mu bude kofar 'yantar da su.

Hatsari Uku Da Ke Fuskantar Labanon

A cikin wannan yanayi, Sheikh Qassem ya jaddada cewa, kasar Lebanon na fuskantar hatsari guda uku na hakika, wadanda suka hada da mamayar da Isra'ila ke yi a kudancin kasar, da "kungiyar ISIS" a kan iyakar gabas, da kuma "Azzaluma Amurka, da ke kokarin mamaye kasar Labanon, tana ba son salladuwa a kanta, da kuma neman kawar da karfinta na motsi da rayuwa".

Your Comment

You are replying to: .
captcha